(ABNA24.com) A cikin bayanin nasa, Muhammad Zakzaky ya bayyana cewa maganarsa tana zuwa a daidai lokacin da mahaifansa suke cikin kuncin da aka saka su, domin kada yin shiru a kan wannan batu yasa mawuyacin halin da suke cikiya ci gaba da kara tsananta, ya zama wajibi ya yi magana.
Ya ce tun bayan da aka dauke mahaifan nasa daga gidan da ake tsare da su zuwa gidan kason Kaduna, jinin mahaifinsa (Sheikh Zakzaky) ya kan sama wani lokaci kuma ya yi kasa.
Haka kuma ita ma mahaifiyarsa (Malama Zinat) tana fama da matsaloli da dama, daga ciki kuwa har da matsalar zubar jinni a cikin kwakwalwarta.
Ya ce a cikin watan Disamban da ya gabata sun samu ganin likitoci daban-daban, kuma sun gudanar da gwaje-gwaje, wani ma ya bayar da umarnin kai su asibiti, amma mahukuntan gidan kason sun musunta hakan.
Ya kara da cewa a ranar 24 ga watan Fabrairu kotu ta bayar da umanin ba su damar ganin likita, haka nan 26 ga fabrairu sun gudanar da wasu gwaje-gwajen, amma duk da wadannan shire-shiye na ganin likitocin da aka yi mgana da su, mahukuntan gidan kaso ba su bayar da dama ba.
Maimakon haka ma mahukuntan gidan kason sun kara saka wasu ka’idoji kan cewa dukkanin abubuwa da aka shirya na ganin likita dole ne sai sun samu amincewa daga na gaba da su da ke a babban birni, da ma wasu ka’idojin na daban, wanda hakan ke nuni da cewa dukkanin kokarin da aka yi, da sauran shirye-shirye kan wannan batu sun rushe kenan.
/129
15 Maris 2020 - 06:43
Lambar labari: 1017534
A jiya ne Muhammad Ibrahim Zaklzaky dan Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran harkar muslunci a Najeriya ya fitar da wani bayani, dangane da halin da mahaifansa suke ciki a gidan kason Kaduna da ake tsare da su.